DA KWAKWALWA AKE TUNANI BA DA TUMBI BA...
Daga Arc Abubakar R Abubakar...
Ganin
yadda ya jajirce, ya maida masu babatu da hargowa cikin duhun rashin
gane ina ya dosa, sai yasa suka koma suna ganin kamar an barsu a kasuwar
da ba kowa ne ko ba ciniki.
Fintinkau
din da yayi musu na zarra a fagen tunani da kuma aiki da basira yasa
suke da shakku akan jama'ar dake tare dasu ko zasu cigaba da yadda dasu.
K0 kuma suna ganin hasken dake tare dashi zai haska zuciyar Al'ummar
dake tare dasu din su guje su.
A
kullum suna ganin haskawar da tauraron shi keyi ke sasu faduwar gaba da
jimami suna ta kwafsawa suna neman mafaka daga wadanda ma basu isa su
basu mafakar ba. Sunyi sunyi su goga mishi baqin fenti a gilasan
Al'ummar dake tare dashi amma har yau hakar su bata kai ga cimma idon
ruwa ba.
Wai shi wancan
ma cewa yayi ai idan har huhun shi na huro mishi numfashi to yayi ya
gama zama shugaba a wannan jaha, niko sai nai dariya nace Ashe ma sai in
kana numfashi, to idan kuma mai duka ya dauke numfashin fa? K0 kuma ga
numfashin amma kana kwance cikin Iarura, K0 kuma ga numfashin amma shi
mai numfashin yafi qarfin ka, to kai zaka dauke numfashin da kanka ko?
Mudai
munga abinda ya zama sabo a idanuwan mu, dan irin abin alkhairan da ya
shuka a lokutan baya cikin Dan qaramin lokaci mu dashi bamu ma taba
tunanin irin hakan ba. Sai dai da yake baka cire rai da ni'imar
ubangiji, aiko saiga ni'imar ta fado mana a daidai Iokacin da muke neman
ta.
Mudai munsan Engr
Nura khalil Alkhairi ne ga jahar katsina da kuma karadua gaba dayan ta.
Dan akan haka yasa mai girma gwamna dallatu mai adalci mai kuma hangen
nesa ya rike shi gam domin ya taimaka masa wajen ci da talakawa gaba.
kuma muna sa ran zamu samu cigaban da bamu taba gani muddin Allah ya
bashi ikon zama sanata mai wakiltan karadua kamar yadda yayi lokacin
PTF.
Karadua ta injiniya Nura khalil ce.
#WeSupportNuraKhalil2019 karadua zone inshaAllah
Arc abubakar R abubakar
Comments
Post a Comment