ENGR MUHAMMAD NURA KHALIL MADUGUN SIYASAR KATSINA DA GWAGWARMAYAR DA YAYI.



Kashi Na 01.
√√√√√√√√√

Lokacinda Engr Muhammad Nura khalil ya shiga jam'iyyar ANPP A 1999,2000-2002 ya taradda jam'iyyar A cikin wani mawuyacin Hali Rashin kudaden Guda narda Ayyukan Yau Da Kullun na jam'iyya sakamakon Rashin mataimaka.

Kwatsam ana cikin wannan Hali Saiga Engr Muhammad Nura khalil ya shigo cikin jam'iyyar tashin Farko yace aje kowace Ward dake cikin katsina Birni Da kauye akama party office Na ward shi zai biya kudin, Haka akaje 361 ko ina aka kama office Engr Muhammad Nura khalil shine ya biya wadannan kudin lakadan ba Ajalanba. 

Sannan yace Aje local Government 34 Kowace akama party office na local Government ya Dunkule kudin ya Basu. 

Har ila Yau, yace Aje Cikin Birnin katsina a Duba office, state party office Ya Dauki Kudi Naira Milliyan Daya da wani Abu tun wancen lokacin da Naira tafi Daraja. 

Engr muhammad Nura khalil Shi kadai yaita Dawainiya da jam'iyyar ANPP a wancen lokacin ko mataimaka babu, Sabida Da akazo maganar Takara Da zabe Engr Muhammad Nura khalil  Shi yasaima Yan takarar sanata Na katsina Form Bakidaya 
Yasaima  
Mannir yakubu Form Din takarar kujerar senator A yankin katsina Zone.

Yasaima Margayi Kanti Bello Form din takarar kujerar sanata na yankin Daura Zone. 

Yazo yankin karadua Zone wallahi Billahil Azeem la ilaha illahuwa yasaima Abu Ibrahim Form Din takarar kujerar Senator Kuma ya Bashi Milliyan 10 Cash Kudin kamfe. 

Sannan yakoma Duk wasu yan takara Na jam'iyyar ANPP Masu Neman Majalisar tarayya Da majalisar Jaha A wancen lokacin Harda (Minister of Aviation)Na Yanzu Hadi Sirika,Sannan Kuma Ya Bisu Da kudin Kamfen Sannan yasaimasu (Tax Clearance) a lokacin Engr Muhammad Nur khalil ya tsayama Sale Jibia yayi (Majority leader)

Shi Yatsayama Musa Adamu Funtua Har suka kai Gaci.
Shi ya tsaya ma Alh Mamuda Wargaji Daga Bakori Local Government. 

Da Lokacin Kamfen ya zo Engr muhammad Nura khalil Shi ya Dauki Nauyin Duk motocin Da aka tara wajen Kamfen Babu wani Dan takara na Sanata, majalisar tarayya da na Jahohi Hatta Dan takarar kujerar shugaban kasa Baikashe ko sisi ba alokacin Engr muhammad Nura khalil shi yasa akayo Bill na kafatanin motocin Da sukaje wajen,kudin Abincinsu, Gurin kwana Da sauran Abubuwan Da Baza a Rasaba. 

Wannnan Shine kadan Daga cikin Hidimar Da Engr muhammad Nura khalil ya yiwa jam'iyyar Apc tun tana ANPP.

Wannan kashi Na farko Ne, sauran sunanan tafe. 
Duk Wanda Baiyadda da Abinda muka fadiba yaje yayi Bincike ko Kuma ya tambayi maigidanshi cewa shin Engr Muhammad Nura khalil ya taima keshi Ko bai taimakeshiba?

Comr Bilyaminu Lawal Funtua

Comments

Popular posts from this blog

BIOGRAPHY OF ENGR. MOHAMMED NURA KHALIL

2019: 40 POLITICAL GROUPS ENDORSE ENGINEER KHALIL FOR KATSINA GOVERNOR