DUK ACIKIN YAN TAKARAR KUJERAR SENATOR NA YANKIN KARADUA ZONE BABU WANDA YAKAI ENGR. MUHAMMAD NURA KHALIL CAN CANTA.































 


Daga Abubakar R. Abubakar

Bayan Kiraye kirayen da Alumna sukai tayi dangane da zaben 2019.yanzu zabi yarage Namu Domin tura shugaba Mai Adalci Domin wakiltar idan kakar zaben 2019 ta karaso. 

Kamar yadda ta Bayyana mun hangi wadansu yan takara duk sun Fiddo makaman yakin neman zabe basu nan basu can sunata tsalle tsalle da hauragiya, sun cika koina da fastoci da bilbod, Babu Mutun daya daga cikin su wanda ya tsaya yayima Alumma kyakyawar magana akan Manufofinshi da Kuma dalilan takarar kujerar senator daya keyi, Domin Alumma Susan cewa tawace hanya zai taimakesu. 


Babu shakka ko kokwanton komawar wadanda suke kyautata rayuwar Alummar dasuka xabesu, Sannan kuma na hango faduwa kasa warwass ga wadanda basu tsinanawa Alummar su komiba. 

Nanda Dan lokaci kadan yan takara zasu fara yawan kanfe Domin neman Alumma, Dazarar Alumma suka fahimci Manufofin Dan takara shikenan, wannan ba Sabon Abu bane dukkan Alummar dasuke taammuli da siyasa sun San haka,Kamar yadda masana sirrin siyasa suke ta magana cewa babu wanda zai iya Fiddo yankin Funtua zone daga cikin halin Kaka nikayi, mutum Mai garta babu kamar Engr Muhammad Nura khalil Domin sun leka koina basuga kamarshiba wannan shi Alummar shine suke kirashi akan Dan girman Allah yazo yataimakemu kuma Allah cikin ikonshi yasa ya Amsa, wanda idan Ka Kalli sauran yan Takarar kujerar senator duka su suka kawo kansu babu wanda ya rokesu su fito, sunfito ne kawai sabida wata boyayyar manufarsu. 


Babu abinda bazan taba mantawa dashi ba Illa wata ranar Assabar ranar da akayi taron Gangamin Amsar Engr Muhammad Nura khalil Na ga taron Alumma, tunbin masoya Engr nura Kalil daga koina afadin jahar nan, dauke da fastoci, da Banoni sun sanya rigunan Engr Nura Kalil suna fadin Sai (Nura )
Abinda yayi matukar burge shugaban jam'iyya NA kasa Mr oyegun da maigirma governor Rtd Hon Aminu Bello Masari sun ga masoya na ban mamaki, Hatta wadanda basu zo wajen sabida Engr Muhammad Nura khalil ba saida suka rikide cikin tafiyar Engr Nura Kalil, musamman Rabin taro yakoma kan Inuwa Baki kyamar kowa. 


Allah mai Baiwa Engr Muhammad Nura khalil bai Ida rukita Filin Polo ba Sai da yafara magana, Hazikine,wajen iya sarrafa luggar harshe da balagar iya magana cikin miliyoyin Alumma Hankalin kowa Yadawo kanshi Kai kace shi kadaine awajen. 

Duk wata kwarewa ta siyasa ya iya tun tuni, sabida yayi takarar Governor local government 34babu inda bai takaba, Yanzu idan Ana maganar takarar kujerar senator NA yankin karadua zone wayafi dacewa yanemi wannan kujerar?  Waya kamata ya zama Sanatanmmu? Waye ya fishi dacewa da cancanta? Waye yafishi wahaltama siyasa da jam'iyyar Adawa?  Waye yafishi hakuri da juriya? Waye yafishi farin jini da son ci gaban Alumna? 
Wannan Amsar Ba awajena take Alummar Karadua Zone su yafi cancanta subada wannan Amsar.

Muna rokon Delegates/Excos du tsaya tsayin daka wajen duba cancanta idan anzo zaben fidda gwani, kusani ku wakilai ne na Alumma kuma ALLAH zai tambayeku abisa wakilcin daya baku, kuzabarwa Alumma Shuwagabanni na gari. Kada wani mai mulki ya siyesu koya zare masu idanu, ko Ayi maku barazanar tsifgeawa kutsaya ku jajirce wajen yin Adalci.

Arc Abubakar R. Abubakar

Comments

Popular posts from this blog

BIOGRAPHY OF ENGR. MOHAMMED NURA KHALIL

ENGR MUHAMMAD NURA KHALIL MADUGUN SIYASAR KATSINA DA GWAGWARMAYAR DA YAYI.

2019: 40 POLITICAL GROUPS ENDORSE ENGINEER KHALIL FOR KATSINA GOVERNOR