DANDAZON MAGOYA BAYA NA KUNGIYOYI DAGA JIHAR KATSINA SUKA NUNA AMINCEWAR INJINIYA NURA KHALIL YA FITO TAKARA A SHEKARAR 2019.

 
 
 

Kungiyoyidaban daban daga jihar katsina sama da guda arbain suna nuna goyon baya da amincewa da injiniya Nura Khalil ya zamanto musu dan Takara a shekarar 2019 bisa tattaunawa da suka Yi a ranar litinin 22 ga watan   janairu 2018 a yankin katsina.
 
Wannan yabon da sakon ya biyo bayan sun hanga sun duba sun ga dacewa da can canta tare da farin jini da gogewa a fannin siyasa da rikon amana don ciyar da yanki gaba.
 
Shugaban kuma jagoran tafiyar magoya Bayan injiniya Nura Khalil  Malam Abubakar Rabiu inda ya bayyana kalamai masu gamsarwa a kasidar Bayan taro da dandazo magoya Bayan Nura Khalil inda suka nuna cewa shi ne ya fi dacewa kuma fitattance dan siyasa a yankin da ya sha gwagwar Maya da adawar siyasa tun shekarar 1999 Wanda ya sha  lashe zaben fidda gwani na jami'iyyar ANNP.
 
 Dan takarar Wanda har yanzu bai bayana aniyyar Sa na tsayawa takarar ba duk da manyan taruka da yake gudana domin aiwatar da aniyyar tasa.
 
Duban magoya baya suka Yi Kira da injiniya Nura Khalil ya fito ya bayyanar da Aniyyarsa ta takarar Gwamnan jihar katsina Ko ya tsaya takarar sanata Mai wakiltar yankin funtua a shekarar 2019 idan Allah ya yadda.
 
Magoya Bayan da suka yi taron sun hada da Engineer Nura Khalil vanguard,katsina state artisans,katsina state youth forum,Nura Khalil mandate promoters of political parties  da sarauran Yan jihar katsina ta dikko dakin Kara.

Comments

Popular posts from this blog

BIOGRAPHY OF ENGR. MOHAMMED NURA KHALIL

ENGR MUHAMMAD NURA KHALIL MADUGUN SIYASAR KATSINA DA GWAGWARMAYAR DA YAYI.

NASHIRYA TSAF WAJAN BADA GUDUNMUWA GA ENGR NURA KHALIL DASHIDA MAIGIRMA GWAMNAN JAHAR KATSINA 2019