TUBALIN GINA SABUWAR KARADUA.






Kamar yadda muketa fuskantar matsaloli iri iri dangane da wannan kasa tamu Mai albarka. 
Hakika idan muka cigaba da tafiya ahaka to nangaba bamu San halin dazamu tsinci kanmmuba Sai dai muita fama da yawan gurace -gurace acikin zuciyar mu wanda bamusan iya adadin gurin mu ba,tunda basuda iyaka. 

Munsani cewa a rayuwa dukkan Dan Adam baka rasashi da guri, da Kuma jarabawar rayuwa iri iri, hatta shi kanshi wannan yanayin da muke ciki wani muhimmin darasine a rayuwar mu, Kamar wata magana da Engr. Muhammad Nura khalil ya yi ne "Duk Dan Adam yanada wani guri da yakeso yaga ya cimmashi,Amma kafin ya cimma wannan gurin saiya jajirce kuma yayi hakuri domin zai ta haduwa da matsaloli iri iri, kuma wannan dolene indai abin Alkairi kakeda gurin kayi "

Bazamu yanke tsammani ba akan cewa watara na matsalolin da wannan kasar take ciki zasu zamo tarihi, tabbas akwana a tashi watarana zamuyu Dariya cikin yardar Allah. 
Kullun gurinmmu shine wannan kasar tamu ta fuskanci Alkibla Mai kyau. 

Akwai hanyoyi dadama dazamu iya mikewa tsaye akansu Dan ganin munsake gina sabuwar katsina Domin katsina itace gatanmmu kuma fatanmmu. 
Katsina garine Mai Da dadden tarihin zaman lafiya, hadin kai da son juna. Amma Yanzu anbar katsina abaya ta bangarori dadama. 

Alamu sun tabbatar da cewa Engr Muhammad Nura khalil zai iya dawoma da katsina martabarta da ta rasa a idon duniya,Amma yadanganta bisa bukatar Alumma akan kiraye kiraye da ake tayi musamman a yankin karadua Don suma suna fatan yazo ya cecesu daga cikin mawuyacin halin da yankin yake.
Tundaga wancen lokacin zuwa Yanzu muna kallon Engr Muhammad Nura khalil a matsayin mutum Mai hakuri, jinkai tausayi da taimakon Alumma,Ilimi da gogewa a bangaren siyasa.,wadannan halayen da sune ake gina Alumma. 

Duk da wadannan nasarori,Cancanta,da tsawon Sanayyar da mukai mashi a harkar siyasa miyasa Bazamu bashi damaba Domin muga irin Kamun ludayinshi da Kuma irin gudun muwar dazai Bamu Idan muka zabeshi? 
Yankin karadua Engr Muhammad Nura khalil yana tareda ku Dari bisa Dari............ 


#Teamnurakhalilmovement. 
#wesupportnurakhalil2019
#Istandwithnurakhalil.

Comments

Popular posts from this blog

BIOGRAPHY OF ENGR. MOHAMMED NURA KHALIL

ENGR MUHAMMAD NURA KHALIL MADUGUN SIYASAR KATSINA DA GWAGWARMAYAR DA YAYI.

NASHIRYA TSAF WAJAN BADA GUDUNMUWA GA ENGR NURA KHALIL DASHIDA MAIGIRMA GWAMNAN JAHAR KATSINA 2019