DA KWAKWALWA AKE TUNANI BA DA TUMBI BA...
Daga Arc Abubakar R Abubakar... Ganin yadda ya jajirce, ya maida masu babatu da hargowa cikin duhun rashin gane ina ya dosa, sai yasa suka koma suna ganin kamar an barsu a kasuwar da ba kowa ne ko ba ciniki. Fintinkau din da yayi musu na zarra a fagen tunani da kuma aiki da basira yasa suke da shakku akan jama'ar dake tare dasu ko zasu cigaba da yadda dasu. K0 kuma suna ganin hasken dake tare dashi zai haska zuciyar Al'ummar dake tare dasu din su guje su. A kullum suna ganin haskawar da tauraron shi keyi ke sasu faduwar gaba da jimami suna ta kwafsawa suna neman mafaka daga wadanda ma basu isa su basu mafakar ba. Sunyi sunyi su goga mishi baqin fenti a gilasan Al'ummar dake tare dashi amma har yau hakar su bata kai ga cimma idon ruwa ba. Wai shi wancan ma cewa yayi ai idan har huhun shi na huro mishi numfashi to yayi ya gama zama shugaba a wannan jaha, niko sai nai dariya nace Ashe ma sai in kana numfashi, to idan kuma...